Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu ya bukaci bankuna da su samar da sunayen barayin abokan ciniki kafin zaben 2019.
Wata sanarwa daga kakakin hukumar EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya bayyana cewa Magu ya sanar da hakan a ranar Talata a jihar Lagas yayin tattaunawa da kungiyar manyan jami’’ai na bankunan Najeriya.
Shugaban na EFCC yace hakan zai taimaka wajen rage yawan cin hanci da rashawa a kasar, inda ya kara da cewa bankuna da daman a kokarin durkushewa a yanzu sakamakon ayyukan barayin mutane.Ya kuma umurci bankuna da su dunga ba hukumar bayanai day a kamata domin taimaka masu wajen aiwatar da ayyukan da rataya a wuyansu.
Magu ya kuma nuna damuwa akan asusu masu zaman kansu a Najeriya, inda yace yan siyasa na iya sheganta damar.
Daga karshe Magu ya bayyana cewa hukumar a shirye take ta taimakawa bankuna wajen dawo da gurbatattun basusukka.
Source :naij hausa
Title :
Yakamata Bankuna Su Bamu Sunayen Barayin Gwamnati - Magu
Description : Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu ya bukaci bankuna da su samar da sunayen barayin abokan ciniki kafin...
Rating :
5