Babban lauyan Najeriya mai lambar girma ta SAN, Femi Falana, ya ce mayar da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiyya ta kasa ya kawo karshen munafunci da makircin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
A jawabin sa, Falana ya bayyana cewar mayar da 12 ga watan Yuni ranar dimokradiyya ya kara tabbatar da sahihancin zaben da tsohon shugaban kasa a mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya rushe saboda mugunta.Babban lauyan ya bukaci gwamnati ta yi amfani da manufar neman yakin zaben marigayi Abiola domin kawo karshen talaucin da ya addabi ‘yan Najeriya.
Falana ya kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kafa tarihi ta hanyar karrama marigayi Abiola da lambar girma ta GCFR tare da mayar da 12 ga watan Yuni ta zama ranar dimokradiyya tare da bayyana cewar hakan ya kara tabbatar da cewar Abiola ne ya lashe zaben shekarar 1993 da gwamnati soji ta soke.
Lauyan ya kara da cewa kamata ya yi bikin ranar dimokradiyya na farko da za a yi wannan shekarar ranar 12 ga watan Yuni, gwamnatin Najeriya ta saki duk wasu mutane da ake tsare da su a gidajen yari ko hukumomin tsaro ba bisa ka’ida ba.
Falana, mai rajin kare hakkin bil’adama ya dade yana kira ga gwamnatin tarayya da ta mutunta umarnin kotu ta saki shugaban mabiya shi’a da gwamnati ke cigaba da tsare shi'a tun shekarar 2016.
Source :naij hausa
Title :
Yadda Buhari Ya Kawo Karshen Makircin Obasanjo - Falana
Description : Babban lauyan Najeriya mai lambar girma ta SAN, Femi Falana, ya ce mayar da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiyya ta kasa ya kawo k...
Rating :
5