A tarihi an taba samun wata karamar yarinya mai shekaru 5 a Duniya da ta haihu. Wannan abu dai tabbas ya faru ne a tsakiyar shekarar 1939 ba wai tatsuniya bane. Sunan wannan yarinya Lina Medina.Lina Medina ta haifi yaron ta ne tana shekara 5 da rabi kacal a Duniya a Kasar Feru.
A lokacin da ta samu juna biyu dai iyayen wannan yarinya sun dauka cewa cuta ce ta samu a cikin ta. Ko da aka je wajen Likitoci sai aka ji labarin juna-biyu.Ba kasafai dai ake samun karamar yarinya irin wannan ta dauki ciki ba, dalilin haka ne ma aka kama Mahaifin ta bisa zargin shi yayi mata ciki.
Da aka yi bincike dai an saki Mahaifin na ta amma dai har gobe babu wanda ya san uban wannan yaron.An radawa yaron da wannan karamar yarinya ta haifa suna Gerardo.
Sai da aka yi aiki a cikin wannan yarinya ake fede ta sannan aka yi zaro jaririn. Wannan dai ya faru ne a Garin Ticrapo da ke Yankin Castrovirrenya na cikin Kasar na Feru a 1939.
Sunan babban Likitan da ya karbi wannan haihuwa kuwa Gerardo Lozada. Kuma yaron da aka haifa ya zo ne bul-bul da nauyi kusan 6.00 lb, haka kuma ai tsawon sa ya haura sentimita 47 watau Inci 18.7.
A tarihi dai an taba samun ‘yan shekara 6 ma ta haihu.A watan azumin nan ne ku ka ji cewa ‘Diyar babban Malamin addinin Musuluncin nan da aka yi a Arewacin Najeriya watau Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ta samu haihuwar yaro namiji.
Source :naij hausa
Title :
Wata Yarinya Ta Haihu Tanada Shekara Biyar A Duniya
Description : A tarihi an taba samun wata karamar yarinya mai shekaru 5 a Duniya da ta haihu. Wannan abu dai tabbas ya faru ne a tsakiyar shekarar 1939 ba...
Rating :
5