Wani labari mai ratsa zuciya da ya auku a garin Kano dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na nuni ne da yadda wata bahaushiyar 'yar asalin Kano din tayi gamo da katar bayan da ta musuluntar da wani baturen Amurka, ta kuma aure shi a karshen satin da ya gabata.
Kamar dai yadda muka samu daga labaran dake ta yaduwa a kafafen sadarwar zamani, ma'auratan na yanzu sun shafe kusan shekaru biyu suna ta zabga soyayyar su a kafar sadarwar zamani ba tare da haduwa da juna ba.
NAIJ.com ta samu cewa bayan sun gama daidaitawa da juna ne dai sai baturen ya nufo Najeriya inda ya sauka a garin Kano ya kuma aure matar sa a wani yanayi mai ban sha'awa da kayatarwa.
Da take karin haske, amaryar ta bayyana cewa tuni daman ita bata boye masa ba cewar ta taba yin aure har sau biyu sannan kuma tana da da amma duk da haka baturen ya amince ya aure ta.
Haka zalika dai ance baturen ya musulunta, yanzu ya canza suna ya zuwa Musa.
Source :naij hausa
Title :
Wata Bakanuwa Ta Musuluntar Da Wani Bature Sannan Ta Aureshi
Description : Wani labari mai ratsa zuciya da ya auku a garin Kano dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na nuni ne da yadda wata bahaushiyar 'y...
Rating :
5