Mun samu labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Alkalin Alkalai na babban Kotun Tarayya a makon nan. Majalisar Dattawan Kasar ta tabbatar da wannan a zaman da tayi a jiya Talata da rana.
Shugaban Kasar ya nada Alkali mai shari’a Adamu Kafarati a matsayin Shugaban Alkalan babban Kotun Tarayyar Najeriya kamar yadda Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana a gaban Majalisa inda ya karanto takardar Shugaban kasar.
Yanzu dai dole sai Sanatocin Kasar sun tantance Alkali Abdul Adamu Kafarati a kafin ya zama takamaiman Alkalin Alkalai na babban Kotun Kasar.
Shugaba Buhari dai yana sa rai Majalisar Dattawan ta amince da wannan mukami da ya bada.
Kafin nan dai Abdul Adamu Kafarati shi ne Mukaddashin Alkalin Alkalai na Kotun inda yake rikon kwarya. Wannan karo Shugaban Kasa Buhari ya nemi Majalisa ta tabbatar da shi a kan wannan matsayi kamar yadda tsarin dokar kasa ta tanada.
A makon nan dai ne wani rikici yake kokarin barkewa tsakanin Shugaban Kasa Buhari da Majalisa inda ‘Yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa su ka sha alwashin tsige Shugaba Muhammadu Buhari a dalilin binciken da ake yi kan wasu manya a Majalisar.
Source :naij hausa
Title :
Wasikan Buhari Zuwaga Saraki
Description : Mun samu labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Alkalin Alkalai na babban Kotun Tarayya a makon nan. Majalisar Dattawan Kasar ta...
Rating :
5