Jiya ne mu ka ji cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kashi a wani zabe da aka yi na Majalisar dokoki a Jihar Oyo.
Abin mamaki dai shi ne ana tunani Jam’iyyar APC mai mulki ce ke da karfi a Jihar.Honarabul Adebo Ogundoyin ne ya lashe zaben kujerar ‘Dan Majalisar dokokin Yankin Gabashin Garin Ibarapa da ke cikin Jihar Oyo.
Jam’iyyar PDP ta taya ‘Dan takarar na ta murnar lashe wannan kujera a zaben da aka yi.Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya taya matashin ‘Dan takarar murnar samun nasarar cin wannan kujera ta Majalisar Jihar.
Adebo Ogundoyin dai Matashi ne mai shekaru 30-da-wani-abu kuma yana da Digiri.An yi zaben ne domin maye gurbin Kakakin Majalisar dokokin Jihar wanda ya rasu kwanakin baya.
Kamar yadda mu ka samu labari ‘Dan takarar na Jam’iyyar adawa Adebo Ogundoyin yayi karatu ne a Jami’ar nan ta Babcock.
Wanda yayi nasara 'Dan uwan Kakakin Majalisar Jihar da ya rasu ne kwanaki watau Marigayi Micheal Apeyamo wanda ya cika yana da shekaru 47. Jami'in zaben Ayodeji Omole ya sanar da cewa Ogundoyin polled ya samu kuri'a 6277.'Dan takara APC a zaben Olukunle Adeyemo ya zo na biyu ne inda ya tashi da kuri'a 4,619 kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.
Kwanaki kun ji cewa wasu manyan Jam’iyyar APC sun koka da abin da ya faru wajen zaben shugabannin Jam’iyyar da aka yi kwanaki a Jihar ta Oyo. PDP kuma dai ta dage cewa dama za ta ba Matasa dama a 2019.
Source :naij hausa
Title :
Wani Matashi Dan Jam'iyyar PDP Ya Doke Dan APC A Jihar Oyo
Description : Jiya ne mu ka ji cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kashi a wani zabe da aka yi na Majalisar dokoki a Jihar Oyo. Abin mamaki dai shi ne an...
Rating :
5