Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na tabbatar mana da cewa za a ci gaba da shirin taron kolin da aka shirya za'a yi tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da takwaran sa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un a Singapore ranar 12 ga watan Yuni.
Wannan labarin dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan shugaban na Amurka ya soke taron a wani yanayin da ya jefa hankulan manyan jami'an diflomasiyya na duniya cikin fargaba da rudani.
NAIJ.com dai ta samu cewa Mista Trump ne ya sake sanar da haka bayan wata ganawar sirri da yayi da wani babban jakadan kasar ta Koriya ta Arewa a dadar mulkin sa na White House.
Jakadan na Koriya ta Arewa mai suna Janar Kom Yong-chol ya mika wa Shugaba Trump din wata wasika ce hannu da hannu daga Shugaban sa Kim Jon-un na Koriya ta Arewa.
Yanzu dai idanuwan duniya da hankulan su sun karkata ne akan yadda tattaunawar tsakanin shugabannin kasashen biyu zata kasance nan da 'yan kwanaki kadan masu zuwa.
Source :naij hausa
Title :
Trump Yayi Amai Ya Lashe
Description : Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na tabbatar mana da cewa za a ci gaba da shirin taron kolin da aka shirya za'a yi tsakanin shu...
Rating :
5