Gwamnatin kasar China ta bayyana cewa a shirye take ta nuna Najeriya da ma sauran kasashen Africa hanyoyin da ta bi ta rage kamfar Talaucin da ya addabe ta a da.Hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Ofishin huldar kasa da kasa na China Xi Yanchun.
Xi ya bayyana hakan bayan da ya karbi bakuncin wakilan ‘yan Jaridar Najeriya a Ofishin nasu (CSCIO) dake Beijing, ya ce kasar China ta zurfafa aniyarta matuka wajen taimakawa Najeriya da ma sauran kasashen Africa domin su dakile tsananin Talaucin da yayi kanta ga kasashen nasu ta hanyar ba su irin samfurin daftarin manhajar da tayi amfani da ita.A yanzu haka dai kasar ta China na shirin fitar da Mutane Miliyan 40 daga cikin Talauci nan da shekarar 2020.
A don haka ina kiran kasashen da su rungumi irin tsarin da China tayi amfani da shi na maganace matsanancin Talauci, domin su ma su yi amfani da shi su kawo karshensa a kasashensu.
"Gwamnatinmu takan tura jami’ai su shiga karkara domin zama a can har na tsawon wasu shekaru, hakan ne yake basu damar gano matsalolinsu da kuma yadda za’a magance su cikin sauki.” A cewar Xi.
Sannan ya kara da cewa, “Wata hanya kuma da suke amfani da ita wajen magance Talaucin ita ce tabbatar da tallafawa wadanda suka cancanta daga karkara domin suyi ilimi Gwamnati ta dauki nauyinsu, hakan shi zai sanya su ma su ji ana yi da su har su shigo ana damawa da su”
.Daga nan ne ya kara kira ga kasashen da su bullo da wani shiri na hadin gwuiwa domin magance tsatsar da Talauci yayi ta hanyar shigowa da kowa a dama tare, kama daga kan Gwamnati da daidaiku da kamfanunuwa da kungiyoyin farar hula da kuma masu zaman kansu.
Irin wannan tsare-tsare su zasu tabbatar da kowa ya dogara da kansa ya kuma kasance ya bayar da tashi gudunmawar wajen kawo cigaba mai dorewa. “A saboda haka kasar China kofar ta a bude take don ganin ta taimakawa sauran kasashen Duniya wajen more rayuwarsu kamar yadda ya kamata” Xi Yanchun ya tabbatar.
Source :naij hausa
Title :
Taimakon Da China Zatayi Wa Nijeriya
Description : Gwamnatin kasar China ta bayyana cewa a shirye take ta nuna Najeriya da ma sauran kasashen Africa hanyoyin da ta bi ta rage kamfar Talaucin ...
Rating :
5