In kun kula, zaku ga iska mai kyau, tafi ruwa ko abinci amfani, ga duk wani mai motsi a doron kasa, shi yasa ma, zaka iya jure kwanaki babu abinci, awanni babu ruwa, amma iska? ko minti daya baka isa ka jure ba babu ita a huhunka.
Wasu lokuta a zamunnan da can, babu takanoloji, babu inji babu boko, don haka tace iska a wurin bacci, kogo ko daki, gida ko makwanci, ya zama wajibi ga jama'a da su sanya furanni masu kyautata da tace iska.
A irin wannan zamani da ake samun kayan zamani kuwa, sai aka gano duk da haka, ababen more rayuwa na birni suna da nasu illolin, don haka har yanzu dai wadanda duniya ko nature ta bayar, sun fi armashi da tsafta.
Wasu cikin tsirran da muka kawo muku a nan, kun sansu, wasu baku sansu ba don babu a yankinku, amma kuna iya gane ganyayyakinsu ko masu kama dasu don adanawa a daka.
Daga cikinsu, akwai masu bada Oxygen, iskar da muke shaqa, akwai kuma masu karawa da kamshi da ma sanyaya daki, wasunsu kuwa, sukan tace gubar CO2 da muke fitarwa yayin numfashi daga daki.Sukan kuma kara ado da ma kawata mazauni kamar falo, tsakar gida, da ma dakin bacci.
Source :naij hausa
Title :
Shukoki Masu Gyara Iska Wanda Ake Sawa A Daki
Description : In kun kula, zaku ga iska mai kyau, tafi ruwa ko abinci amfani, ga duk wani mai motsi a doron kasa, shi yasa ma, zaka iya jure kwanaki babu ...
Rating :
5