Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mutumin dake da cikakken dattaku da kwarewa wajen iya tafiyar da Najeriya, amm fa mutanen dake zagaye da shi baragurbi ne.
Sani ya bayyana haka ne a yayin hira da gidan talabijin na Channels, inda yace ya san Buhari tun kafin ya zama shugaban kasa, suna tare a jihar Kaduna, kuma ya tabbatar cewar mai gaskiya ne, amma akwai bukatar ya kawar da mutanen dake tare da shi a yanzu.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Sanatan yana kokawa kan yadda Buhari baya daukan mutanen da suka dace a tafiyarsa, haka zalika yace Buhari ya gaza wajen magance kashe kashen da ake yi a arewacin kasar nan.
“Gwamnati ta gaza karara wajen hana kashe kashen da ake yi a Arewacin Najeriya, don haka kai ya rabu, kuma yan Najeriya basa ganin kansu a matsayin yan Najeriya, sun fi ganin kansu a matsayin yan kudu, yan Arewa, Musulmai ko Kirista. Ina jiye ma Buhari saboda wannan matsalar kashe kashen za ta bata masa suna a wajen yan Najeriya.
” Inji shi.Sai dai a wani kaolin, Shehu Sani ya yaba da namijin kokarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen yaki da ta’addanci, da kuma yadda take tafiyar da akalar tattalin arzikin kasar, duk da halin da ake ciki.
Daga karshe ya bayyana cewa majalisar dattawa bata da laifi cikin rashin tabbatar da shugaban hukuma EFCC, Ibrahim Magu, inda yace hukumar tsaro ta sirri, DSS, ne ta kai musu rahoton dake nuna Magu ba shi da gaskiya.
Source :naij hausa
Title :
Shawarar Shehu Sani Zuwaga Buhari
Description : Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mutumin dake da cikakken dattaku da kwarew...
Rating :
5