Jaridar Naij ta samu cewa tuni dai wani bangare daga jam'iyyar APC din da suka bar jam'iyyar PDP a gabanin zaben 2015 suka fara wani yunkurin ballewa daga jam'iyyar.
Sai dai mun samu cewa jagororin bangarorin biyu sun yi wata ganawa a makon da ya gabata inda aka yanke shawarar kafa wani kwamitin da zai lalubo hanyar sasanci a tsakanin su.
Daga baya ne ma muka samu cewa bangarin na sabuwar PDP sun zayyana sharuddan su 4 da suke so a cika masu kafin su zauna a jam'iyyar:
1. Janye kararrakin da aka shigar a kan Sanata Abubakar Bukola Saraki.
2. Bai Honorable Yakubu Dogara da Dr Rabiu Musa Kwankwaso wasu kujeru a zaben shugabannin jam’iyyar APC a jihohinsu.
3. Kawo karshen muzgunawa da EFCC ke yi wa wasu daga cikinsu.
4. Sa sufeto Janar na ‘yan sanda da ya gurfana gaban majalisar dattawa.
Source :naij hausa
Title :
Sharudan Su Kwankwaso Zuwaga Jam'iyyar APC
Description : Jaridar Naij ta samu cewa tuni dai wani bangare daga jam'iyyar APC din da suka bar jam'iyyar PDP a gabanin zaben 2015 suka fara wani...
Rating :
5