A wani mataki na yunkurin kawo sauye-sauye a kasar ta, karon farko mun samu cewa kasar Saudiyya a hukumance ta fara baiwa mata lasisin yin tuki a kasar ta daga ranar 24 ga watan nan na Yuni da muke ciki mai zuwa.
Kamar yadda muka samu, mahukunta a kasar sun wasu mata ne a matsayin matakin farko domin fara koya masu yadda za su yi tukin tare kuma da fara basu lasisin yin hakan.
NAIJ.com ta samu cewa lamarin dai ya dauki hankulan al'umma da dama musamman ma musulmi a dukkan fadin duniya biyo bayan wani faifan bidiyo daya bayyana a kafafen sada zumunta kunshe da yanda ake dankawa wata mata lasisin fara tukin nata.
Kafrin yanzu dai kasar Saudiyya na zaman kasa daya tilo a Duniya dake da dokar hana mata tuki.
Source :naij hausa
Title :
Saudiyya Tafara Baiwa Mata Lasisin Yin Tuki
Description : A wani mataki na yunkurin kawo sauye-sauye a kasar ta, karon farko mun samu cewa kasar Saudiyya a hukumance ta fara baiwa mata lasisin yin t...
Rating :
5