Mun samu labari dazu daga Daily Trust cewa Hukumar man fetur na Najeriya na NNPC ta kawo wani sabon tsari da zai taimaka wajen rage barna da kuma kawo kazanta a wuraren da ake aikin mai a Kasar.
Shugaban Kamfanin NNPC Dr. Maikanti Baru ya bayyana cewa NNPC za ta rage kazantar da aka saba wajen aikin man fetur tare da dabbaka wasu tsare-tsaren da su sa a rage watsar da dattin mai. Baru ya bayyana wannan ne jiya a Abuja.
Rahoton ya zo mana cewa wani babban Jami’in kula da aikace-aikace na Hukumar NNPC watau Injiniya Saidu Muhammadu ne ya wakilci Maikanti Baru a wajen wannan taro na musamman a babban ofishin NNPC da ke babban birnin Tarayya.
NNPC tace za ta tafi da tsarin da ta kawo na rage kazanta a Kasar wanda hakan zai taimaka wajen kare lafiyar al’umma. Robobi dai na da illa ga ruwa da kuma kasar da jama’a ke amfani da ita don haka NNPC tace za ta yi gyara a aikin ta.
Hukumar na NNPC tayi wannan taro ne a jiya Talata da ta ke Ranar bikin muhalli na Duniya. NNPC za tayi amfani da fasahar zamani domin ganin an rage kazanta da kuma gurbata wuraren da al’umma su ke zama domin gudun cutuwa.
Source :naij hausa
Title :
Sabon Tsarin NNPC Kan Harkar Mai
Description : Mun samu labari dazu daga Daily Trust cewa Hukumar man fetur na Najeriya na NNPC ta kawo wani sabon tsari da zai taimaka wajen rage barna da...
Rating :
5