Wani mai wa'azin addinin musulunci dan kasar Kuwaiti, Mubarak Al-Bathali ya fadi karar cewa rashin yin azumi da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammed Salah ya yi a ranar 26 ga watan Mayu ne ya janyo masa fushin Allah a wasar karshe da suka buga a Kiev.
Mohammed Salah dai ya yi gwagwarmayar neman kwallo ne da mai taimakawa wajen tsaron gida na kungiyar Madrid, Sergio Ramos wanda hakan ta haifar masa jin rauni a kafadarsa kuma daga baya ya fice daga wasar bayan mintuna 30 da farawa saboda radadi.
Da farko dai, an ruwaito cewa Mohammed Sallah zai yi azumi a ranar wasan karshe ta cin gasar kwararu da za'ayi a birnin Kiev amma daga bisani sai likitan kungiyar Liverpool ya tabbatar da cewa ba zai yi azumi a ranar ba.
Ya dai ajiye azuminsa a ranar 26 ga watan Mayun 2018 amma bai samu ikon kammala karo na farko a wasar ba kuma daga baya kungiyarsa ta Liverpool tayi rashin nasara inda kungiyar Real Madrid ta doke Liverpool din da 3-1.
Sai dai malamin kasar Kuwaiti, Mubarak al-Bathali ya ce Salah ya yi zunubi saboda ajiye azumi da ya yi a dalilin kwallon inda ya kara da cewa bashi da kwakwaran dalili a addinance na ajiye azumin.
"Allah ne ya hukunta shi saboda ya ajiye azumi, kuma zai fuskanci hukuncin da zai biyo baya."Kada kayi tunanin cewa dabara da kokari ne ke tafiyar da rayuwar musulmi, rayuwa na hannun Allah ne kuma shi ya ke juya ta yadda ya so.
"Wata kila ma raunin da ka samu alkhairi ne gare ka," kamar yadda mai wa'azin kasar ta Kuwaiti ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Source :naij hausa
Title :
Raunin Salah Hukuncin Allah Ne Kan Ajiye Azumin Da Yayi - Malamin Islama
Description : Wani mai wa'azin addinin musulunci dan kasar Kuwaiti, Mubarak Al-Bathali ya fadi karar cewa rashin yin azumi da dan wasan kungiyar kwall...
Rating :
5