A yau, Lahadi, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a shirye yake ya karrama gayyatar da hukumar da ‘yan sanda tayi masa dsa zarar takardar gayyatar ta same shi.
Kazalika, Saraki ya musanta cewar akwai wata alaka dake tsakanin sa da mutanen da ake zargi da aikata laifin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari ya lamuncewa shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya , Ibrahim K. Idris, kama Saraki bayan gabatar masa da shaidar samun hannun Saraki a cikin aiyukan ta’addanci, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.
Ayau, Lahadi, ne hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar wasu daga cikin wadanda ta kama dangane da batun fashin bankunan garin Offa sun ambaci sunan Saraki da na gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, a matsayin mutanen dake daukar nauyin aiyukan sun a ta’addanci.
Kakakin shugaban kasa da na hukumar ‘yan sanda sun ki cewa komai a kan wannan batu da kuma ganawar shugaba Buhari da shugaban na ‘yan sanda ta ranar juma’a.
Da yake jawabi cikin snarwar da mai Magana da yawun sa, Yusuph Olaniyonu, ya fitar, Saraki y ace alakanta shi da fashi wani makirci ne kawai na bata masa suna.
Source :naij hausa
Title :
Na Amince Yan Sanda Su Kama Saraki - Buhari
Description : A yau, Lahadi, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a shirye yake ya karrama gayyatar da hukumar da ‘yan sanda tayi ...
Rating :
5