Jam'iyyar APC ta garin Iwo, dake jihar Osun, ta karbi sama da mutum 1,000 wadanda suka canja sheka daga jam'iyyar PDPJam'iyyar APC ta garin Iwo, dake jihar Osun, ta karbi sama da mutum 1,000 wadanda suka canja sheka daga jam'iyyar PDP.
Shugabannin jam'iyyar ta APC sune suka karbi masu canja shekar, a lokacin da suke gabatar da wani taro da wani shugaban gargajiya na yankin Iwo ya hada, Cif Diekola Ismail Adefowope, taron da aka gabatar a babban dakin taro na garin Iwo.Wani tsohon jigo a jam'iyyar PDP shine ya jagoranci kungiyar masu canja shekar, Mista Ajao Muritala Olaleye, yace sun yanke hukuncin barin jam'iyyar ne saboda jam'iyyar PDP ba ta da wani hadin kai, sannan kuma jam'iyyar tana yin abu kawai domin cigaban kanta bana al'umma ba.
Taron wanda ya samu halartar mutane masu tarin yawa, wadanda suka hada manyan 'yan siyasa na yankin, shugabannin gargajiya, kungiyoyin siyasa, mawaka da kuma shugabannin dalibai.
A bayanin da yayi, gwamnan jihar ta Osun, Rauf Aregbesola ya jinjinawa Adefowope da kokarin da yayi, sannan kuma ya bada tabbacin cewar jam'iyyar zata kula da wadanda suka canja shekan kamar yanda ya kamata.
Source :naij hausa
Title :
Mutane Da Dama Sun Canza Sheka Sa PDP Zuwa APC
Description : Jam'iyyar APC ta garin Iwo, dake jihar Osun, ta karbi sama da mutum 1,000 wadanda suka canja sheka daga jam'iyyar PDPJam'iyyar A...
Rating :
5