Duk da irin jin dadi da alfarmar dake cikin mulki musamman ma mulki irin na Najeriya, to sai gashi da yawa daga cikin masu mulkin suna korafin cewar akwai matsaloli masu dunbin yawa a tattare da mulkinBa sosai aka fiya jin masu mulki suna korafi akan irin matsalolin da suke fuskanta ba, to sai dai kuma a wata hira da aka yi da gwamnan jihar Bauchi Mohammed A Abubakar ya lissafo matsaloli har guda biyar wadanda ya nuna cewar suna ci mishi tuwo a kwarya.
1. Nisanta ga iyali
Aiki ne wanda zai dauke ka daga 'ya'yanka da sauran 'yan uwanka."Da akwai wani abu da ya taba faruwa dani, nayi tafiya nayi wajen sati biyu bana nan, ina da dana wanda watanninsa wajen biyar ko shida, ina dawowa dana zo na dauke shi ya zura min ido, sai ya dauke kansa yana neman yayi kuka saboda bai gane ko wanene ni ba."
2. Rashin samun isasshen bacci da dare
Taro na tsakar dare shima yana da illa matuka.
3. Rashin samun lokacin kanka
Rashin samun isasshen lokaci. Kamar ni a rayuwata ina son abubuwan motsa jiki koda safe koda yamma a duk tsawon rayuwata. Amma a yanzu sai naje na zauna a ofis na kasa samun lokacin gabatar da wannan abubuwan nawa."Kamar irin su kwallon Golf ina bugawa, yanzu yau anyi wajen wata biyar ban samu damar yi ba."
4. Rashin burge jama'a
Aiki ne wanda duk iyawarka sai wani yayi korafi, musamman yanzu da aka samu na'ura mai kwakwalwa da kuma yanar gizo (internet), dole ne kaje ka samu wani ya kalubalance ka, kuma ba tare da yasan menene ma gaskiyar maganar ba.
5. Hulda da 'yan jarida
Ku 'yan jarida abokanan aiki ne, to amma a lokuta da dama zaku zauna da mutum zai fadi magana, ku kuma sai kuje kubi wata hanya ku juya maganar ku fadi san ranku, a karshe sai maganar ta kawo matsala.
Source :naij hausa
Title :
Matsalolin Yin Mulki A Nijeriya - Gwamnan Bauchi
Description : Duk da irin jin dadi da alfarmar dake cikin mulki musamman ma mulki irin na Najeriya, to sai gashi da yawa daga cikin masu mulkin suna koraf...
Rating :
5