Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta sha caccaka a wurin kungiyar shugabannin kiristoci ta kasar watau Christian Association of Nigeria (CAN) bisa zargin da suka yi na cewa an tambayi wadanda suka rubuta jarabawar daukar aikin 'yan sanda game da harshen larabci.
Ita dai kungiyar ta Christian Association of Nigeria (CAN) ta bayyana matsayar ta ne a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun shugaban ta na kasa baki daya Rabaran Samson Ayokunle a ranar Alhamis din da ta gabata.
NAIJ.com ta tuna cewa a karshen satin da ya gabata ne dai hukumar shirya jarabawar shiga jami'a a Najeriya watau JAMB ta yi wa masu sha'awar shiga aikin dan sanda a Najeriyar jarabawa a cibiyoyin dake fadin kasar nan.
A wani labarin kuma, Kimanin kasa da wata daya bayan da wata daliba ta fallasa wani malamin ta a jami'ar Obafemi Awolowo University, dake jihar Osun da ya nemi ya kwanta da ita, wata budurwar ma daga jami'ar garin Legas ita ma ta kara fallasa wani malamin.
Ita dai wannan budurwar daga jami'ar Legas din wadda aka boye sunan ta saboda dalilai na tsaro ta ce sunan Farfesan da ya ci zarafin nata shine Olusegun.
Source :naij hausa
Title :
Kungiyar Kiristoci Ta Caccaki Gwamnatin Buhari
Description : Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta sha caccaka a wurin kungiyar shugabannin kiristoci ta kasar watau Christi...
Rating :
5