Ibrahim Idris, babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa yam aka majalisar dattijai da shugaban ta, Bukola Saraki, gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja bisa bayyana shi a matsayin makiyin dimokradiyya da bai dace da rike wani ofishi na shugabancin jama’a ba da majalisar ta yi.
A yau ne, Alhamis, 7 ga watan Yuni, Idris ya sami sahalewar babbar kotun karkashin mai shari’a, John Tsoho, domin shigar da karar majalisar da kuma Bukola Saraki domin fara sauraro a gaban ta.
A ranar 9 watan Mayu ne majalisar dattijai ta bayyana cewar IG Idris bai dace ya zama jagoran jama’a ba saboda makiyin siyasa ne. Majalisar ta bayyana hakan ne bayan IG Idris ya ki amsa gayyatar da tayi masa a karo na uku.
Source :naij hausa
Title :
Kotu Tasake Baiwa IG Daman Damke Saraki
Description : Ibrahim Idris, babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa yam aka majalisar dattijai da shugaban ta, Bukola Saraki, gaban wata babbar kotun ...
Rating :
5