Babban kotun jihar Kaduna ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Ramallan Yero.
An dai tsare Ramalan Yero ne tare da wasu jami'an gwamnati uku wandanda ake tuhuma da laifin wawure kudaden al'umma lokacin da ya ke mulkin jihar.
Idan baku manta ba alkalin kotun, Jastis Muhammad Shua’aibu ya bada umurni a makon jiya cewa a garkame tsohon gwamnan da wasu uku a gidan yari har ranan 6 ga watan Yuni.
An gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Abubakar Gaya Haruna; tsohon sakataren gwamnatin jihar, Hamza Ishaq, da tsohon ministan wuta, Nuhu Somo Wya.
Ana tuhumar Yero da laifin almundahanar kudi N700 miliyan da kuma yaudara.
Sai dai tuhumar da ake yiwa tsohon gwamnan ya janyo cece-kuce tsakanin al'umma inda wasu ke ganin kawai bita da kulli ake masa.
Source :naij hausa
Title :
Kotu Tabada Belin Lamaran Yero
Description : Babban kotun jihar Kaduna ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Ramallan Yero. An dai tsare Ramalan Yero ne tare da wasu jami'an gwamn...
Rating :
5