Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie tayi gargadin cewa rungumar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ba zai kare barayin yan siyasa ba.
Lauretta tayi ba’a ga barayin gwamnatin ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu.
Da take maida martani akan hukuncin dauri da wata babban kotun tarayya ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Mista Jolly Nyame, a ranar Laraba, Onochie ta yi gargadin cewa hukuncin da akayi masa ya nuna cewa APC ba aljanar masu laifi bane.
Sannan kuma Onochie tayi ba’a ga jam’iyyar PDP a shafin Facebook inda tace sun kasa daure tsohon gwamnan.
Idan zaku tuna a baya NAIJ.com ta tattaro cewa wata babbar kotun tarayya ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba shekaru 14 a gidan yari ba tare da tara ba.
Hakazalika a yanzu haka an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero a gaban kotu bayan tuhumar amdame kudi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi masa tare da wasu yan siyasa.
Source :naij hausa
Title :
Komawa Jam'iyyar APC Bazai Ceceku Ba - Lauretta
Description : Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie tayi gargadin cewa rungumar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ba zai kare b...
Rating :
5