Mamaki ya mamaye Duniyar ƙwallon ƙafa a yau Alhamis tun bayan da Mai horas da ƙungiyar ƙwalon ƙafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya sanar da hukuncinsa na barin ƙungiyar.
Zinedine Zidane dai ya bayyana wannan hukuncin ne yayin wani taron manema labarai, sai dai har yanzu babu wani taka maiman dalilin da yasa ya ajiye aikin. Sai kawai ya ce ƴan wasan suna da bukatar sabuwar muryar mai horaswa.
Sai dai "Ya bayyana cewa samun nasarar lashe gasar LaLiga ta kakar wasannin shekarar da ta gabata shi ne babban abinda da yake tutiya da shi.
"Amma ya shaida cewa shi kansa ya san abu ne mai wahala kuma da yawa ba zasu ji dadin hakan ba, tun da rabuwa ba Mutuwa ce ba.
Zai kasance a koda yaushe kusa da kungiyar don alakar zumunci, kasancewar soyayyar dake tsakaninsa da kungiyar da kuma ƴan wasanta tare da magoya Bayanta.
Source :naij hausa
Title :
Kocin Realmadrid Ya Ajiye Aikin Sa
Description : Mamaki ya mamaye Duniyar ƙwallon ƙafa a yau Alhamis tun bayan da Mai horas da ƙungiyar ƙwalon ƙafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya sanar d...
Rating :
5