Mun leka gidan kwallon kafa inda mu ka kawo maku wasu mutum 3 da ake sa ran za su maye gurbin tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane wanda a rana tsaka yace ya tashi daga Kungiyar bayan ya lashe kofin Zakarun Turai.
1. Arsene Wenger
Shekaru kusan 10 da su ka wuce Real Madrid ta nemi tsohon Kocin Arsenal Wenger amma ya ki zuwa Sifen. Yanzu dai Wenger ya bar Arsenal kuma ba mamaki yana da sha’awar kwallo har yanzu don haka yana iya komawa Real Madrid.
2. Mauricio Pochettino
Kocin Kungiyar Tottenham yana cikin wadanda ake tunani Real Madrid za su nema ya canji matsayin Zinedine Zidane. Pochettino yayi abin a zo-a gani a Ingila don haka wasu ke ganin cewa Real na iya neman sa.
3. Guti
Guti tsohon ‘Dan wasan Real Madrid ne kamar Zidane kuma yayi aiki a matsayin Mai taimakawa Kocin Kyngiyar a baya. Yanzu haka Guti yana horas da Kananan ‘Yan wasan Real Madrid kuma yana abin a yaba.
Source :naij hausa
Title :
Kocin Da Ake Tsammanin Zai Karbi Realmadrid
Description : Mun leka gidan kwallon kafa inda mu ka kawo maku wasu mutum 3 da ake sa ran za su maye gurbin tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane wanda...
Rating :
5