Fitaciyyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta ja hankalin mabiya shafinta na zumunta kna su hankalta da masu bude shafuka na bogi da sunanta.
Jarumar ta wallafa wani shafi na bogi da aka bude da sunan ta wanda ke rokon jama'a da su tallafa da kudi domin tallafawa marasa karfi.
Ta nisantar da kanta daga shafin tare da yin kira ga jama'a da su kauracewa ire-iren shafukan bogi masu bukatar kudi daga masu bibiyan ta.wannan yana daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwa yadda ake yawan bude shafukan bogi da sunan su tare da neman kudi daga jama'a.
A baya NAIJ.com ta kawo maku hotunan yadda jarumar tayi rabon kayayyakin abinci na azumi da kayan sallah ga marasa karfi a farkon watan Ramadana.
Babu mamaki wannan halin alkhairi na jarumar ne ya janyo hankulan mutane har suke son yin amfani da damar wajen yaudarar mutane da sunanta.
Source :naij hausa
Title :
Jan Hankalin Hadiza Gabon Zuwaga Mabiya
Description : Fitaciyyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta ja hankalin mabiya shafinta na zumunta kna su ...
Rating :
5