Masana da likitoci sun dade ta ganowa cewa shan tabar cigari na yiwa huhun dan-adam lahani tare da janyo cutar daji sai dai a yanzu wata sabuwar bincike ta kara bankado wasu ilolin da tabar cigarin ke yiwa dukkan jikin dan-adam.
Kwarariya likita Maria Ocampo mai kula da asibitin bincike a kan illar tabar cigari da wasu ababen masu kamanceceniya dashi ta ce shan tabar cigari yana lalata dukkan tsokar da ke jikin dan-adam ba wai huhu kawai ba duk da cewa ciwon daji na huhun shine kan gaba ajalin mashaya tabar cigari.
"Babu tsokar da tabar cigabari bai yi wa lahani saboda shi hayakin tabar yana yawo a jikin dan adam tare da iskar da muke shaka kuma babu yadda za'ayi dan adam ya rayu muddin ya shakar iska," inji Ocampo.Campo ta yi wannan bayanin ne a jiya 31 ga watan Mayu wanda duniya ta ware a matsayin ranar yaki da shan tabar cigari.
Ranar na wannan shekarar anyi mata lakabi da "Cigari na karya zukata"Ocampo ta cigaba da bayani inda tace idan mutum ya zuka tabar cigari, hayakin zai cakwude da iskar da yake shaka wanda kuma zai hade da jininsa sai dai a maimakon jinin ya zagaya da iskar mai kyau (oxygen) zuwa dukkan tsokar da ke jikinsa, gurbataccen iskar (Carbonmonoxide) ce za ta kasance ta gurbata jinin kuma wannan gurbataccen jinin ne zai karade jikinsa har zuwa kwakwalwa da kafafu da sauransu."Hakan yasa idan ka lura da labba da hanayen masu shan tabar cigari za kaga sunyi duhu.
Wannan alama ce ta rashin isashen iska mai kyau wato Oxygen," inji ta.Bayan gurbataciyar iskar carbon monoxide da ke cikin tabar cigarin, akwai kimanin kwayoyin Chemical 4,000 zuwa 7,000 kuma sama da 60 cikinsu da janyo cutar daji wato Cancer.Campo ta kara da cewa jikin mashaya tabar cigari na kokarin samar da karin jini wanda hakan ke sanya jinin ya yi kauri sosai wanda hakan na hana jinin zagayawa cikin hanyoyin jinin wanda dama sun matse saboda illar cigari. Hakan ne ke haifar da bugawar zuciya.
Ta kuma ce mata masu shan tabar cigari sun fi kamuwa da cutar dajin mahaifa da na nonuwa, su kuma maza sun fi kamuwa da cutar dajin koda da Prostrate kuma dukkaninsu suna saurin tsufa.
Sai dai ta kuma ce da zarar mutum ya dena shan tabar cigarin, jikinsa zai fara samun waraka yana kokarin kawar da kwayoyin cutar inda ta shawarci masu son dena shan tabar su rika shan ruwa isashe tare da samun barci da kuma motsa jiki da wasannin da ba zai kaisu ga shan cigabarin ba.
Source :naij hausa
Title :
Illolin Da Sigari Keyi A Jikin Dan Adam
Description : Masana da likitoci sun dade ta ganowa cewa shan tabar cigari na yiwa huhun dan-adam lahani tare da janyo cutar daji sai dai a yanzu wata sab...
Rating :
5