Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa Gwamnan jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya nada Alhaji Audu Sule Katagum a matsayin sabon mataimakin sa.
Kamar dai yadda muka samu, Gwamnan ya bayyana wannan nadin ne lokacin da yake ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a gwamnatin sa a gidan gwamnatin jihar.
NAIJ.com ta samu cewa shi dai Alhaji Audu Sule Katagum an nada shi ne domin ya maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan Injiniya Nuhu Gidado da yayi murabus a watan jiya.
A wani labarin kuma, Babban jakadan kasar Ghana a Najeriya Mista Rashid Bawa ya nesanta kasar sa da kalaman da aka ruwaito wai cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce shugaban kasar Ghana Nana Akuffo-Addo ne ya fada game da harkar tsaron Najeriya.
Da yake karin haske game da lamarin, jakadan kasar Ghana din ya fada a ranar Juma'ar da ta gabata cewa tsohon shugaban kasar ya datsi kalaman shugaban kasar ta Ghana ne amma ba haka yake nufi ba.
Source :naij hausa
Title :
Gwamnan Jihar Bauchi Ya Maye Gurbin Mataimakin Gwamnansa Dayayi Murabus
Description : Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa Gwamnan jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan Gwamna Mohammed Abdull...
Rating :
5