Wata sabuwar jarumar fina finan Kannywood da tauraruwarta ke haskawa a yanzu, Amina Amal ta bayyana hakinan gaskiyar dangantakarta da fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango, inji rahoton jaridar Aminiya.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaita Amal wanda ta baro kasarta na Asali, kasar Kamaru da dawo Najeriya da nufin shirin Fim, ta bayyana cewa akwai soyayya a tsakaninta da Adam Zango, amma fa ba irin soyayyar da ake tsammani ba, face soyayyar yaya da kanwarsa.
“Soyayya tana nan sai karuwa take, soyayyar ya da kanwa muke yi ma juna, domin ya dauke ni a matsayin kanwars, ni kumana dauke shi a matsayin yayana, kaga kenan babu wata soyayya a tsakanin Yaya da kanwa.” Inji ta.
Haka zalika jarumar ta musanta batun da yadawa na cewa wai tana soyayyar saurayi da budurwa da Abu Sarki, inda tace Maigidanta a harkar Fim, kuma sun shaku da juna sosai, amma fa ma soyayya suke yi ba.
Sai dai jarumar tace a yanzu bata samun walwala, tun bayan wani shiga da ta yi kasuwar barci dake garin Kaduna, inda masoya suk mamaye ta kowa na son daukar hoto da ita, kowa na son ganinta, daga nan wani wani ya janyo mata hannu, numfashinta ya dauke kamar za ta mutu, da kyar aka kwaceta.
Da take karin haske kan bahallatsar da ta faru a kwanakin baya kan yadda wani hotonta sanye da matsatstsun kaya suka bayyana a shafinta na Instagram, sai tace wata kawarta, kuma aminiyarta ce ta daura hoton ba tare da saninta ba, sakamakon ta san lambobin sirrin wayarta.
Daga karshe jarumar tace har yanzu burinta a Kannywood bai kammala cika ba, saboda bata kai matsayin da take son ganin ta kai ba, don kuwa burinta shi ne ta zama kamar Hadiza Gabon ko Fati Muhammad.
Source :naij hausa
Title :
Gaskiyan Abinda Ke Tsakani Na Da Zango - Amina Amal
Description : Wata sabuwar jarumar fina finan Kannywood da tauraruwarta ke haskawa a yanzu, Amina Amal ta bayyana hakinan gaskiyar dangantakarta da fitacc...
Rating :
5