Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya yi ma wani jajirtaccen jami’in Dansanda, Ahmad Abdulraman karin girma zuwa mukamin kwamishinan Yansanda, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto.
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Hayatuddeen Lawal Makarfi ne ya bayyana haka a shafinsa, inda ya tabbatar da labarin karin girmar da hukumar Yansandan Najeriya ta amince a yi ma Dansanda Ahmad.
Shi dai Ahmad shi ne jami’in Dansanda daya tilo da ya yi fice wajen gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani a watan Azumin Ramadan a jihar Kaduna, inda yake gabatar da Tafsirin a shelkwatar Yansandan jihar Kaduna.
A baya NAIJ.com ta kawo muuku rahoton cewar Kwamishina Ahmad Abdulrahman yace ya samu kwarin giwar shiga aikin Yansanda ne daga mariyagin Shehin Malami, Abubakar Mahmud Gumi, bayan rikicin addini da ya kaure a zangon kataf na jihar Kaduna.
Da fatan Allah yayi ma sabon mukaminsa albarka, tare da amfanar da al’umma gabaki daya.
Source :naij hausa
Title :
Dan Sandan Dake Gabatar Da Tafsiri Yasami Katon Girma
Description : Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya yi ma wani jajirtaccen jami’in Dansanda, Ahmad Abdulraman karin girma zuwa mukami...
Rating :
5