Mun samu labari cewa babban Jam’iyyar adawa a Najeriya watau PDP ta yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sa hannu da yayi kan kudirin nan na ‘Not Too Young to Run’ a jiya. PDP tace a 2019 kuma za ta tafi da Matasa.
A jiya da rana ne Shugaban Kasar ya rattaba hannun sa a kan wannan kudiri da ya zama doka a Fadar Shugaban Kasa.
Hakan dai zai bada dama Matasa har ‘Yan shekara 25 su tsaya takarar kujerar Majalisar Tarayya a Najeriya.
Sakataren yada labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa watau Kola Ologbondiyan ya yabawa Shugaban Kasa Buhari da ya sa hannun-sa inda ya kira wannan mataki da aka dauka a matsayin nasara ga Matasan Kasar nan baki daya.
Kola Ologbondiyan ya kuma yabawa kokarin Honarabul Tony Nwulu wanda ya fara kawo kudirin gaban Majalisa. Haka kuma Jam’iyyar dai ta kuma yi kira ga Matasa da su yi amfani da wannan damar da aka samu a Najeriya.
Jam’iyyar ta kuma jinjinawa Matasan da su ka dauki wannan abu a ka har aka dace ya zama doka. Sai dai PDP tace Jam’iyyar APC ba ta taka rawar gani wajen ganin wannan kudiri ya samu shiga ba saboda ‘Dan PDP ya kawo maganar.
Ologbondiyan ya bayyana cewa ka da Shugaba Buhari ko APC su rika jin cewa su ne su kayi ruwa-da-tsaki wajen aikin wannan kudiri. Ologbondiyan yace Shugaban Kasar ya rattaba hannun sa ne bayan an kammala komai a Majalisa.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa PDP Ta Jinjina Wa Buhari
Description : Mun samu labari cewa babban Jam’iyyar adawa a Najeriya watau PDP ta yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sa hannu da yayi kan kudirin na...
Rating :
5