Bayan suka da majalisu ke ta sha kan kin rage shekarun takarar Sanata da na gwamna, a yau mataimakin shugaban majalisa ya bayyana dalilansu na kin rage wadannan kujeru duk da hakan shi samari suka fi so.
A cewarsa dai, Ike Ikweremadu, shekarun sanata da na shugaban kasa dole su zo kai-daya, saboda akwai lokutan da za'a sami gibi a kujerar mulki, kuma shugaban majalisa a senate shi ne zai iya maye gurbin kujerar ko da na wucin gadi ne.
A batun takarar gwamna kuwa, cewa yayi in aka kai takarar zuwa masu shekaru 30, ba lallai ace dan shekara talatin ya kai wani munzalin iya tafiyar da jiha ba, ko ma ace ya tara wasu ilimummuka na mulki da guudanarwa.
A bisa dalilin haka suka ga 35 ita ce mafi dacewa a ce ana iya takara a jihohi.Sauran kujeru kuwa, an rage shekaru biyar biyar, harda ta shugaban kasa.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Bamu Rage Shekarun Takaran Gwamna Da Sanata Ba - Majalisar Dattijai
Description : Bayan suka da majalisu ke ta sha kan kin rage shekarun takarar Sanata da na gwamna, a yau mataimakin shugaban majalisa ya bayyana dalilansu ...
Rating :
5