Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cika wani tsohon alkawari da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, marigayi janar Sani Abacha ya daukar ma wani Baturen kasar Holland, inji rahoton NAIJ.com.
A shekarar 1996 ne dai kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta lashe kyautar zinariya a gasar kwallon kafa na Olympic a karkashin jagorancin mai horas da kungiyar, Bonfere Jo, wannan lamari yayi ma Abacha dadi, inda ya yi alkawarin bashi kyautar gida a Abuja.
Haka aka yi ta tafiya har shekarar 1998, inda Abacha ya rasu ba tare da ya cika ma Jo alkawarinsa ba, gwmanatocin baya suka zo suka shude, basu cika ma wannan Baturen Alkawarinsa ba, sai a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni Buhari ya cika wannan alkawari.
A yayin da yake mika masa makullan gidan, Ministan ayyuka, gidaje da lantarki, Babatunde Fashola ya bayyana godiyar gwamnati ga Bonfere, sa’annan ya bashi hakurin tsawon lokacin da ya kwashe yana jiran cikar wannan alkawari.
Shi ma a nasa jawabin bayan ya karbi makullan gidan ciki uku da aka gina shi a Gwagwalada, Jo ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin Najeriya da ta cika masa wannan alkawari.
“A matsayina na wanda ya taimaka ma Najeriya wajen lashe tagulla a Olypimc da gasar cin kofin Afirka, ina yi ma Super Eagles fatan alheri a wasannin da zasu fafata na gasar cin kofin Duniya a Rasha.” Inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Ya Cika Wani Alkawarin Da Abacha Ya Dauka
Description : Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cika wani tsohon alkawari da tsohon shugaban kasa na mulkin soja...
Rating :
5