Mun samu labari cewa jiya ne wani babban Jami’in Hukumar zabe na Kasa watau INEC ya cika-baki inda yace ba zai yiwu a murde zabe yanzu a Najeriya ba saboda gyare-gyaren da aka kawo.
Wannan babban Jami’i na Hukumar zaben na kasa yayi watsi da koke-koken da Jam’iyyar adawa ta PDP ke yi na cewa sai yadda fadar Shugaban Kasa Buhari tayi da Hukumar. Jami’in na INEC yace sam babu kanshin gaskiya a wannan maganar na PDP.
INEC tace ta gudanar da zabuka dabam-dabam bayan zaben 2015 kuma Jam’iyyar PDP tayi nasara a da-dama daga cikin su don haka maganar ace ana hada baki tsakanin Hukumar zaben na INEC da Jam’iyyar APC mai mulki ba gaskiya bane.
Haka kuma Hukumar zaben na kasa tace fasahar da aka kawo na zamani ya bada damar al’umma su zabi wanda su ke so. Fasahar da aka kawo a 2015 dai na tantance masu kada kuri’a shi ne yayi maganin makudin da ake yi a zabe inji INEC.
Sai dai INEC tace ba za a sake kirkirar wasu tashoshin zabe ba daga nan har 2019 domin kuwa yin hakan zai kara kawo matsala ne kurum. Sai dai kuma za a raba wasu wuraren zaben gida 2 a kara yawan akwatin zabe domin a rage cinkoso.
Source :naij hausa
Title :
Babu Halin Murdiya Ko Magudi A Zaben 2019 - INEC
Description : Mun samu labari cewa jiya ne wani babban Jami’in Hukumar zabe na Kasa watau INEC ya cika-baki inda yace ba zai yiwu a murde zabe yanzu a Naj...
Rating :
5