A daidai lokacin da guguwar zaben 2019 ke kara gabatowa, Ministar dake kula da harkokin mata, kuma yar fadar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Aisha Alhassan wacce aka fi sani da Mama Taraba tayi tsokaci akan zabe mai zuwa.
Ministar ta jaddada cewa ko shakka bata yi akan cewa jam’iyyar APC mai mulki ce zata ci gaba da mulkar Najeriya har illa ma sha Allah.A cewarta rikicin da am’iyyar ke fama da ita a halin da ake ciki ba wani sabon abu bane a harkar siyasa.
Ta kara da cewa daga lokacin da jam’iyyar ta gudanar da zaben shugabanninta na kasa toh babu shakka zata iya tunkarar kowace jam’iyyar siyasa a 2019.
A halin da ake ciki, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.
Ta jaddada cewa kowa ya san cewa ita ce ta lashe zaben gwamnan jihar ta Taraba ba don zagon kasa da aka shirya ba.
Source :naij hausa
Title :
APC Zata Yi Mulki Har Illa Masha Allah - Mama Taraba
Description : A daidai lokacin da guguwar zaben 2019 ke kara gabatowa, Ministar dake kula da harkokin mata, kuma yar fadar tsohon mataimakin shugaban kasa...
Rating :
5