Gwamna Henry Seriake Dickson ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta shiga cikin rudu iri-irin don haka ma yace ko kadan babu yadda za ayi Jam’iyyar mai mulkin kasar tayi nasara a zaben 2019.
Henry Seriake Dickson ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa Fidelis Soriwei yace APC ba za ta iya lashe zabe mai zuwa ba. Gwamnan ya bayyana wannan ne lokacin da yake jawabi a Garin Yenagoa a Jihar Bayelsa.
Gwamnan ya nuna cewa Jam’iyyar APC tana cikin rudu ne a yanzu inda rikicin yau dabam kuma na gobe dabam. Gwamna Dickson yace wasu ‘Yan APC da-dama yanzu su na dawowa jirgin Jam’iyyar PDP a Jihar sa domin su tsira.
A cewar Gwamnan dai ko a lokacin zaben 2015, Jam'iyyar APC ba ta iya yin nasara a Jihar Bayelsa ba duk da cewa kuwa Jam’iyyar ke rike da kasar.
Gwamnan yace alkawuran karya kurum APC ke yi wa mutane kuma ba za su kai labari ba.Sai dai Gwamnan yace ana kokarin kakkabe takardun Ma’aikatan Jihar Bayelsa domin karawa wasu matsayi wanda hakan ya jawo koke-koke daga mutanen Jihar sa. Gwamna Dickson yace shi ma bai ji dadin yadda hakan ya kasance ba.
Source :naij hausa
Title :
APC Bazata Ci Jihata Ba - Dickson
Description : Gwamna Henry Seriake Dickson ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta shiga cikin rudu iri-irin don haka ma yace ko kadan babu yadda za ayi Jam’iyya...
Rating :
5