Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya da ke tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na nema su yi baram-baram da ‘Yan uwan su game da rikicin ke kokarin barkewa tsakanin Shugaban Kasar da Majalisa inda su kace su na goyon bayan Shugaban ban kasar har gobe.
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yana fama da wani bincike a hannun ‘Yan Sanda wanda hakan ta sa jiya Majalisun Kasar su kayi wani zaman hadaka na musamman inda har aka cin ma matsayar cewa dole a takawa Shugaba Buhari burki
.Sai dai wasu daga cikin ‘Yan Majalisar wadanda su ka nuna goyon bayan su ga Shugaba Buhari ba su amince da wannan mataki da aka dauka ba. Honarabul Abdulmumin Jibrin (APC/Kano) ya fitar da jawabi a madadin sauran ‘Yan uwan sa a jiya da yamma.
Jibrin yace ba dukkanin Majalisa ta ke goyon bayan matsayar da aka cin ma a jiya ba na cewa za a tsige Shugaban Kasa.
‘Dan Majalisar yace Sanatocin da su ka yi magana a wajen kusan duk ‘Yan PDP ne sai dai babu wani 'Dan APC da ya sa baki saboda gudun rigima.
Honarabul Jibrin wanda kwanaki aka dakatar da shi daga Majalisar yace su na tare da yakin da Shugaban Kasa Buhari ya ke yi da rashin gaskiya kuma su ka shawarci Takwarorin su a Majalisar Kasar da ke da kashin laifi a wajen Hukuma su je su wanke kan su.
Source :naij hausa
Title :
Ansami Rabuwan Kan 'Yan Majalisa Game Da Tsige Buhari
Description : Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya da ke tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na nema su yi baram-baram da ‘Yan uwan su game da rikicin ke kokari...
Rating :
5