Jami’an hukumomin tsaron Najeiriya da suka hada da jami’an Soji, Yansanda da na hukumar DSS sun samu nasarar dakile shigo da wasu dimbin alburusai zuwa Najeriya, kamar yadda rahoton jaridar Rariya ta bayyana.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu, inda jami’an tsaro suka yi ram da wasu Tireloli dake dauke da alburusai fiye guda dubu dari uku, 300,000, sun nufo Najeriya akan iyakar kasar Bini da Najeriya.
Sai dai majiyar ta bayyana cewa direbobin motocin, da sauran masu kokarin shigo da alburusan gida Najeriya sun ranta ana kare, ma’ana jami’an tsaron basu samu nasarar cafke ko daya daga cikinsu ba.
A wani labarin kuma, Dakarun Sojin Najeriya dake aikin kakkabe ragowar yan ta’addan Boko Haram dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar halla yan ta’adda guda uku tare da ceto mutane tara.
Bugu da kari wasu Sojojin Najeriya guda biyar sun gamu da ajalinsu a wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai musu a wani kauye dake karamar hukumar Gwoza, sai dai suma yan ta’addan sun yi asarar mayaka da dama.
Source :naij hausa
Title :
Ankama Wani Tirela Makil Da Alburusai Zai Shigo Nijeriya
Description : Jami’an hukumomin tsaron Najeiriya da suka hada da jami’an Soji, Yansanda da na hukumar DSS sun samu nasarar dakile shigo da wasu dimbin alb...
Rating :
5