Gwamnatin jihar Plateau ta tabbatar da kamuwar wasu Mutane biyu da mummunar cutar nan ta Kyandar Biri a yankin karamar hukumar Shendam ta jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Kunden Deyin ne ya shaida hakan yayin da yake tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), cewa wannan shi ne karon farko da aka samu tabbacin bullar cutar a jihar.
Kwamishinan ya shaidawa NAN faruwar wannan lamari ne yau Alhamis a garin Jos. Ya ce an samu cutar a jikin wasu Mutane biyu da suka zo daga birnin Fatakwal na jihar Rivers domin neman magani.
Deyin ya ce da farko dai daya ne ya fara kamuwa kafin daga bisani ya shafawa gudan, dukkanninsu dai an basu magani a asibitin koyarwa na Bingham. Kuma yanzu haka cibiyar dakile manyan cutuka masu hadari ta jihar na cika da bincike don kiyaye yaduwar cutar.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa alamomin cutar Kyandar Birin iri daya ne da na cutar Kyanda amma sai dai nata tafi tsanani. Sai dai ya bayyana cewa asali cutar a jikin dabbobi ake daukarta kafin daga bisani idan Mutum ya kamu ya gogawa dan uwansa Mutum idan sun yi cudanya.
A don haka ne Deyin ya gargadi masu farautar dabbobin daji kamar Bera, Dage, Kurege da kuma Birrai da dai sauransu, domin masu ta'ammali da su na cikin hadarin kamuwa da kwayar cutar.
Sannan ya bukaci jama’a da su kai rahotan bullar cutar amai da gudawa da duk wata irin cuta da ta feso a ciki da basu gane ko wacce ba ce.
Source :naij hausa
Title :
Anagano Cutar Kyandar Biri A Jihar Plateau
Description : Gwamnatin jihar Plateau ta tabbatar da kamuwar wasu Mutane biyu da mummunar cutar nan ta Kyandar Biri a yankin karamar hukumar Shendam ta ji...
Rating :
5