Shahararren mawakin siyasar nan da aka fi sani da Dauda Kahutu Rarara, sanar da cewa nan bada jimawa ba zai kira taron manema labarai, domin ya sanarwa da jama'a matsayinsa akan zargin da ake yi masa na cewar yayi sama da fadi da kudin kungiyar mawakan yankin arewa sama da naira miliyan 100.
Rararan ya sanar da hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa Al-Ameen Afandaj a lokacin da yake tattaunawa da majiyar mu a ranar Talatar data gabata.
Mawakin ya bayyana cewa nan bada jimawa ba zai kira taron kungiyar mawakan arewan, sannan kuma bayan an kammala taron zai kira taron manema labarai domin yayi musu cikakken bayani akan irin zargin da ake yi masa akan kudin.
"A yanzu haka Rarara ba zai ce komai ga al'umma ba, amma bayan an kammala taron kungiyar mawaka, to zamu gayyaci taron manema labarai, inda shi Rararan da kansa zai yi musu bayani dangane da hatsaniyar dake cikin batun kudin," inji Alfandaj.
Source :naij hausa
Title :
Zan Wanke Kaina Kan Zargin Da Ake Min - Rarara
Description : Shahararren mawakin siyasar nan da aka fi sani da Dauda Kahutu Rarara, sanar da cewa nan bada jimawa ba zai kira taron manema labarai, domin...
Rating :
5