Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyar shi ta samar da aikin yi ga matasa 500,000 nan da shekarar 2020 wanda hakan zai taimaka wajen rage rashin aikin yi dake addabar al'ummar kasar nan.
Kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta maida hankali akan bangarorin habaka tattalin arziki wanda suka hada da noma da kiwo, sufuri, wutar lantarki da iskar gas.
A zantawa da manema labarai a yau, a wurin taron murnar ranar damokaradiyya wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, yace wadannan bangarorin sun fitar da shirye-shirye masu yawa na saka hannayen jari da samar da aiyukan yi na kusan dala biliyan 22.5 wanda zai samar wa mutane 500,000 aikin yi zuwa 2020.
"Mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar da shirin N-Power inda aka samar wa da wadanda suka gama makarantun gaba da sakandare aiyukan yi.
Shugaban kasar yace a halin yanzu matasa 200,000 sun samu aikin yi sannan an zabi 300,000 domin fara basu aiki nan ba da dadewa ba a cikin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.Bayan haka, mutane 20,000 da basu gama makaranta ba an zabe su don su fara shirin N-Build tare da hadin guiwar National Automotive Design and Development Council and the Council of Registered Builders of Nigeria.
Shugaban kasan ya tabbatar da cewa mulkin shi ya samu nasarar tabbatar da walwalar matasan kasar nan kuma zai cigaba da hakan.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Samar Da Aiki Wa Matasa 500,000 A Kasar Nan - Muhammadu Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyar shi ta samar da aikin yi ga matasa 500,000 nan da shekarar 2020 wanda hakan zai taimaka waj...
Rating :
5