Mun samu rahoton cewa kasar Saudiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kasar Vatican inda zata fara coci-coci saboda mabiyya addinin Kirista da ke zaune a kasar ta Saudiyya kamar yadda Breitbart ta wallafa.
Rahotton yace babban sakataren kungiyar kasashen musulmi 'Muslim World League', Sheikh Mohammed bin Abdel Karim Al-Issa ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar tare da shugaban 'Pontifical Council for Inter-religious Dialogue' na kasar Vatican, Cardinal Jean-Louis Tauran.
Kafan yadda labaran na Breitbert kuma ta ruwaito cewa maraba da kasar ta Saudiyya keyi da al'adu da addinan sauran mutanen duniya na da nasaba da kokarin rage dogara a kan man fetur a matsayin jagaban tattalin arzikin kasar.
A yarjejeniyar da kasashen biyu saka rattaba hannu a kai, kasashen biyu zasu kafa wata kwamitin hadin gwiwa mai wakilai biyu daga bagarorin biyu domin su cigaba da tsara yadda za'a cinma nasarar aikin.
An kuma ruwaito cewa kwamitin za ta rika gudanar da taron ta ne sau daya a kowanne mako inda za'a rika yin taron a birnin Rome da kuma ko wane gari da kasar Saudiyya ta zaba.Kawo yanzu, kasar Saudiyya ce kawai kasar larabawa da ba ta da coci ko guda kamar yadda rahoton ya bayyana.
Hakan yana da nasaba da akidar Wahabiyyanci da kasar ke kai wanda ya haramta gudanar da wasu addinan da ba musulunci ba.
Source :naij hausa
Title :
Za'a Gina Coci Na Farko A Saudiyya
Description : Mun samu rahoton cewa kasar Saudiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kasar Vatican inda zata fara coci-coci saboda mabiyya addinin ...
Rating :
5