Babbar hadaddiyar kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ta sha alwashin cigaba da yi wa gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari zanga-zangar kin jini a harabar majami'un su a dukkan fadin kasar nan.
Wannan dai bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar a wata fira da yayi da wakilin majiyar mu inda ya bayyana cewa kiristocin kasar nan sun gaji da yadda jami'an tsaro ke yi wa matsalar rashin tsaro rikon sakainar kashi suna bari ana kashe su kamar kaji a wuraren ibadar su.
NAIJ.com ta samu cewa da aka tambayi shugaban na Kiristoci ko me yasa ba su fitowa yin zanga-zangar a saman tituna sai ya ce suna tsoron kar lamarin ya gagari kundila shi yasa.
A wani labarin kuma, Haddadiyar hadakar nan ta tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo da ta kuduri aniyar fatattakar shugaba Muhammadu Buhari daga mulki a zaben 2019 mai zuwa ta shirya tsaf domin ayyana jam'iyyar da za su goya wa baya.
Wannan matakin dai da hadakar ta dauka kamar yadda muka samu, ya biyo bayan kasa cimma daidaito da jam'iyyar SDP da Cif Obasanjo din ya nemi a yi.
Source :naij hausa
Title :
Yanzu Muka Fara Yiwa Buhari Zanga Zanga - Kiristocin Nijeriya
Description : Babbar hadaddiyar kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ta sha alwashin cigaba da yi wa gwamnatin tarayya...
Rating :
5