Da yawa daga cikin Musulmai basu san an yi yakoki da dama cikin watan Ramadana a zamanin sahabbai da wadanda suka biyo bayansu.
Daga yakin Fatahu Makkah zuwa yarjejeniya Baqt, da kuma yakin Badar. Amma a yau, jaridar NAIJ.com zata kawo muku yakoka 4 wadanda Musulmai suka samu gagarumin nasara a cikin watan Ramadana.
1- Yakin Badar: Yakin da yafi shahara kuma yaki na faro da Musulmai sukayi a tarihi ya faru ne a watan Ramadana, shekara 2 bayan Hijran manzon Allah ﷺ daga Makkah zuwa Madina.
2-Yakin Tabuk 8 AH: Duk da cewan ba’ayi fito na fito ba wannan yaki, Musulmai sun samu gagarumin nasara yayinda rundunar 30,000 karkashin jagorancin manzon Allah ﷺ suka tafi yakan Romawa.Amma da suka isa, aboka adawa sunyi kasa a guiwa basu fito filin daga ba.
3- Yakin Ain Jalut: An yi wannan yaki ne shekara 658 bayan hijra inda sojin Musulmi suka karfin Mongolawa da sukayi kokarin lalata kasashen Musulmai. Miliyoyin Muslmai sunyi shahada a wannan yaki.
4-Yakin Hattin: An yi wannan yaki ne a shekarar 583 bayan hijra yayinda arnan suka yai kasashen Musulmai kuma suka kwace Kudus. Bayan yakin Hattin, musulmai karkashin jagorancin Salahuddenil Ayyubi suka kwato Kudus.
Source :naij hausa
Title :
Yakin Musuluncin Da Akayi Cikin Watan Ramadana
Description : Da yawa daga cikin Musulmai basu san an yi yakoki da dama cikin watan Ramadana a zamanin sahabbai da wadanda suka biyo bayansu. Daga yakin ...
Rating :
5