A wani labari mai ban mamaki, dake fitowa daga kasar Afirka ta Kudu, an sami wata daliba da aka sanya wa akalla dala miliyan daya a asusunta na banki bisa kuskure, inda ake kokarin sanya mata 'yan daloli na tallafi da basu taka kara sun karya ba.
Sai dai maimakon ta maido wa da gwamnati kudin, $1.1m, Sibongile Mani, mai shekaru 28, daliba a jami'ar Walter Sisulu University da ke Eastern Cape province, wata jiha a kasar, kawai sai ta hau kashe kudinta inda har ta ci $63,000 daga kudin.
A cikin kudin dai, N40,000 ($110) ce kawai tata, agajin gwamnati ga dalibai marasa na hannu, amma kafin ma'aikatar da ta tura kudin ta ankare, tuni har ta sai waya, kayan sawa, ta kuma shirya casu da dalibai da abokai.
A ranar talata ne aka kamo budurwar aka kuma garzaya da ita kotun majistare don fuskantar hukuncin sata da almubazziranci, sai dai kamar ba'ayi uzuri ba, domin wa zai ga zunzurutun kudi daga gwamnati ya mayar mata?
Source :naij hausa
Title :
Wata Daliba Ta Hallaka N365m Daga Kudin Da Aka Sanya A Asusunta Bisa Kuskure
Description : A wani labari mai ban mamaki, dake fitowa daga kasar Afirka ta Kudu, an sami wata daliba da aka sanya wa akalla dala miliyan daya a asusunta...
Rating :
5