Wata matashiyar budurwa mai shekaru 18 a duniya ta shaidawa wata kotu dake Ikeja a jihar Legas cewar, mahaifin ta, Folorunso Oluwaseuyn; mai shekaru 52, ya shafe tsawon shekaru hudu yana tilasta mata yin lalata da shi.
Matashiyar, da ba a bayyana sunan ta ba, ta bayyana cewar mahaifin nata ya fara yi mata fyade tun tana da shekaru 12 lokacin da ta koma gidan sa dake unguwar Ikorodu a Legas da zama.
Saurari Rohuto Mun Akan Yanda Mahaifin Ta Yamata
Da take bayar da shaida a gaban alkalin kotun, Sybil Nwaka, matashiyar tace, “ni da ragowar ‘yan uwana hudu muna zaune ne a daki daya a wani gidan haya.
Watarana mahaifina ya kira ni tare da shaida min cewar nono na yafi na ‘yar uwa ta girma, a saboda haka zai zuke min abinda ya fito a ciki.
A wannan ranar ne ya fara tilasta min yin lalata da shi lokacin ina aji 2 makarantar sakandire.”
Matashiyar ta kara da cewar, ta shaidawa ‘yar uwa ta abinda ya faru amma babu abinda zata iyayi a kan hakan.
Sannan ta cigaba da cewa, “haka ya cigaba da yin lalata da ni yana bani ruwan gishiri da sukari.
Duk kokarina na dakatar da shi bai yi aiki ba, sai yace min wai “ko Allah ya sani bashi da mata”, sannan kuma wai ba zai samu kudin da zai dauki nauyin dawainiyar mu ba idan bai kwanta da ni ba.”
Mai shari’a Nwaka ya daga sauraron karar ya zuwa ranar 21ga watan Yuni, 2018.
Title :
Video: Yadda Mahaifina Ya Shafe Tsawon Shekaru 4 Yana Lalata Danii – Wata Matashiya
Description : Wata matashiyar budurwa mai shekaru 18 a duniya ta shaidawa wata kotu dake Ikeja a jihar Legas cewar, mahaifin ta, Folorunso Oluwaseuyn;...
Rating :
5