A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan sanda a Jihar Gombe suka gurfanar da wani mutum mai suna Sama’ila Zakari mai shekara 50 kuma dan asalin garin Deba da ke karamar Hukumar Yamaltu Deba a jihar a gaban Kotun Majistare ta 3 da ke BCJ, a garin Gombe bisa zarginsa da yi wa ’yarsa (an sakaye sunanta) mai shekara 15 fyade har ta samu ciki.
Da akawun kotun Sani Yarima yake karanta masa laifin da ake zarginsa a kamar yada yake kunshe a takardar bayanan farko na ’yan sanda (FIR), ya ce a ranakun 2 da 8 ga watan Fabrairun bana da misalin karfe 10 na dare wanda ake zargin ya dauki ’yar tasa ya kai ta dakin matarsa ba tare da son ranta ba ya yi mata fyade.
Mai gabatar da karar ya ce yanzu haka yarinyar tana dauke da cikin wata biyu da ake zagin mahaifin da yi mata.
Ya ce hakan ya saba wa sassa na 390 da 282 na kundin laifuffuka da hukuncinsu na Final Kod.
Da Alkalin Kotun Mai shari’a Daurabo Suleiman Sikam ta juya waiwayi wanda ake zargin, Sama’ila Zakari, ya musanta zargin da ake yi masa.
Kalli Video Hiran Su
Daga nan sai dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Bako Shekari, ya nemi kotun ta dage sauraron karar zuwa gaba don bai wa ’yan sanda damar su kammala bincikensu.
Alkalin Kotun Mai shari’a Daurabo Sulaiman Sikam, ta dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga Mayun nan tare da ba da umurnin a tura wanda ake zargin zuwa kurkuku zuwa ranar da za a ci gaba da sauraron karar.
Title :
Video: An Gurfanar Da Uba A Kotu Kan Zargin Yi Wa ’Yarsa Cki
Description : A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan sanda a Jihar Gombe suka gurfanar da wani mutum mai suna Sama’ila Zakari mai shekara 50 kuma dan as...
Rating :
5