Mun samu daga majiyar mu ta Rariya cewa shahararren malamin nan, shugaban mazhabar darika a Najeriya kuma fitaccen mai tafsirin al'qur'ani mai girma Sheikh Dahiru Bauchi ya zama gagarabadau a duniyar tafsiri biyo bayan wasu muhimman tarihai da ya kafa a fagen har uku.
Malamin dai yana bin salon Tafsirin Al-qur'ani ne da tsari na fassara Kur'ani da Kur'ani, fassara Kur'ani da Hadisin Manzon Allaah SallalLaHu AlaiHi Wa AliHi Was Sallam, fassara Kur'ani da maganganun Sahabai da Tabi'ai da magabatan Bayi na kwarai.
Kamar dai yadda muka samu, a bana ne fitaccen malamin Sheikh Dahir Usman Bauchi da ke zama a garin Kaduna ya cika shekaru 67 yana gabatar da Tafsirin Alqu'ani.Ya fara Tafsirin Kur'ani a watan Ramadan na Shekarar 1951.
Haka mai dai kuma a wannan azumin na bana ne Sheihin Malamin ya cika shekaru 54 yana gabatar da Tafsirin Al-qur'ani da ka ba tare da duba takarda ba.Wani tarihin da shehin malamin ya kara kafawa kuma shine a bana ya cika shekaru 39 yana tafsirin al'qur'ani mai girma a Birnin Kaduna.
Haka ma dai kamar yadda muka samu daga majiyar ta mu, fitaccen malamin a wannan shekarar ne ake sa ran zai yi tafsirin Al-qur'ani mai girma har sau uku a rayuwar sa.
Source :naij hausa
Title :
Tarihin Da Sheikh Dahiru Bauchi Ya Kafa Akan Tafsirin Alkurani
Description : Mun samu daga majiyar mu ta Rariya cewa shahararren malamin nan, shugaban mazhabar darika a Najeriya kuma fitaccen mai tafsirin al'qur...
Rating :
5