Rundunar Sojin Amurka da ta Najeriya sun tattauna akan harkar tsaro da kuma yadda Najeriya zata cigaba da samun makaman yaki don kawo karshen ta'addancin a kasar Najeriya.
Shuwagabannin rundunonin Sojin sunyi taro suma. Wannan na nuin watakil a sami isowar sojin na Amurka yankin da Boko HAram ta addaba don kawo karshen lamarin da ya kusa shekaru 1o ana fafatawa.
Janar Dunford, shugaban rundunonin Sojin Amurka, shi yayi ma Janar Abayomi Olonisakin, Chief of Defence na Najeriya masauki a Pentagon, babbar tashar tsaro ta Amurka.
A Najeriya dai, jama'a na sa rai sojin turawa zasu zo su agazawa sojojin Najeriya don karas da ta'addanci, duk da cewa a da, lokutan da ta'addanci ya addabi Iraqi da Afghanistan samarin arewa sun sunfi goyon bayan su Osama da Zarqawy.
Source :naij hausa
Title :
Sojoji Na Sabon Shiri Kan Ta'addanci
Description : Rundunar Sojin Amurka da ta Najeriya sun tattauna akan harkar tsaro da kuma yadda Najeriya zata cigaba da samun makaman yaki don kawo karshe...
Rating :
5