Mun samu labari a Ranar Laraban nan cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya watau Bukola Saraki ya kai ziyara har dakin da ‘Yan wasan Super Eagles su ke kwana a Abuja domin yi masu sallama.
Abubakar Bukola Saraki ya kai wa ‘Yan kwallon na Najeriya da ke shirin tafiya zuwa Kasar Rasha domin cin Gasar kofin Duniya na bana ziyarar da ba su yi tsammani ba.
Bukola Saraki ya yabawa ‘Yan wasan Kasar da irin kokarin da su ke yi.Sanata Bukola Saraki ya kuma jinjinawa kokarin Kyaftin din Najeriya John Mikel Obi na jagorantar Kungiyar ta Super Eagles salin-alin.
Saraki yace Mikel Obi da ‘Yan wasan na sa ba su kokawa da irin karancin sakayyar da ake yi masu.
Shugaban Majalisar Dattawan yace yana bibiyar Super Eagles kuma ta tabbata cewa yanzu Kungiyar a dunkule ta ke. Saraki yace ‘Yan Najeriya za su marawa ‘Yan wasan baya a Gasar inda ya ba su gudumuwar kudi har Naira Miliyan 18.
Haka kuma dai Sanatan Kasar ya yabawa kokarin Gernot Rohr wanda shi ne babban Jami’in da ke kula da Super Eagles.
A makon nan dai Najeriya ta yi kunnen doki da ta kara da Kasar Congo a Garin Ribas.
Source :naij hausa
Title :
Saraki Yakai Ziyaran Bazata Wa Yan Wasan Super Eagles
Description : Mun samu labari a Ranar Laraban nan cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya watau Bukola Saraki ya kai ziyara har dakin da ‘Yan wasan Supe...
Rating :
5