Wani na hannun damar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai suna Injiniya Kailani Mohammed ya bayyana cewa su Saraki da Kwankwaso da ma dukkan 'yan tawagar su ta 'yan Sabuwar PDP wadanda suka koma jam'iyyar APC a gabanin zabukan 2015 sun riga sun gama yanke shawarar barin APC.
Sai dai kuma makusancin na shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa ficewar ta su daga jam'iyyar ta APC ba zata shafi kudurin tazarcen na shugaba Buhari a zaben 2019 ba domin kuwa talakawa na tare da shugaban kasar.
NAIJ.com ta samu cewa Injiniya Kailani ya bayyana cewa kuma duk da ganawar da shugabannin daga sabuwar PDP da sukayi da mataimakin shugaban kasa, amma rahotanni na nuna cewa basu gamsu ba.
A wani labarin kuma, Fitaccen dan siyasar na dake zaman tsohon dan majalisar wakilai da kuma majalisar dattijai kuma dan asalin jihar Kaduna, Sanata Baba-Ahmad ya yi kaca-kaca da kurarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na cewa tana yakar cin hanci da rashawa.
Sanatan a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu ta Daily Trust ya bayyana cewa yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasar ke wakar yana yi tamkar bita-da-kulli ne kawai domin cin zarafin wasu adawa da shi.
Source :naij hausa
Title :
Saraki Da Tawagar Sa Sun Yanke Shawarar Barin APC - Kailani Muhammed
Description : Wani na hannun damar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai suna Injiniya Kailani Mohammed ya bayyana cewa su Saraki da Kwankwaso da m...
Rating :
5