Shahararren dan wasan kwallon kafar nan wanda tauraruwar shi take haskawa a yanzu, Mohammed Salah, ya isa kasar Spain domin cigaba da karbar magani dalilin raunin da yaji a lokacin da suka kara wasan karshe na cin kofin zakarun turai tsakanin kungiyarsa ta Liverpool da kuma kungiyar Real Madrid.
Salah wanda ya tafi birnin Valencia na kasar Spain, yaki ya saurari manema labarai a lokacin da suke ta kokarin ganin sunyi masa tambayoyi.
'Yan jaridar na kasar Spain sun nemi su san ko dan wasan zai iya buga wasan gasar cin kofin duniya, sannan kuma sun so su tambaye shi ko yana ganin da gangan ne Sergio Ramos ya ji masa ciwo.
Sergio Ramos wanda shine yayi sanadiyyar jiwa Salah ciwo, yayi gaggawar wallafa wani sako a shafinsa na yanar gizo wato Twitter, inda yake yiwa Salah fatan samun lafiya cikin gaggawa.
An tabbatar da cewar fiye da mutane 500,000 suka goyi bayan a hukunta Ramos a shafin su na koke na yanar gizo petition.org, da zargin cewar Ramos yaji wa Salah ciwo da gangan ne.
Source :naij hausa
Title :
Salah Yatafi Spain Neman Magani
Description : Shahararren dan wasan kwallon kafar nan wanda tauraruwar shi take haskawa a yanzu, Mohammed Salah, ya isa kasar Spain domin cigaba da karbar...
Rating :
5